'An yi kutse a komfutar Hillary Clinton'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dai alakanta masu kutsen da kasar Russia

Hukumomin tsaro a Amurka sun ce an yi wa wata kwamfuta kutse wadda 'yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton ta yi amfani da ita.

Manajojin gangamin yakin neman zaben Hillary su ma sun ce masu kutsen sun samu bayanai bayan da suka shiga kwamfutar.

Da ma dai tun farko, kwamitin da ke tara kudin harkokin zaben 'yar takarar ta jam'iyyar Democrat, ya ce an yi wa kwamfutocinsu kutse domin neman wasu bayanai.

Kafafen watsa labarai na Amurka sun ce mutanen da ake zargi da aikata kutsen suna da alaka da hukumomin leken asiri na kasar Russia.

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka, FBI, ta ce tana tattara bayanai dangane da kutsen.

A makon da ya gabata, a wani yanayin na kutse mai alaka da Russia, shafin fallasar nan na Wikileaks ya fitar da wasu dubban bayanai da aka sato su daga adireshin imail na jam'iyyar Democrat.

Wasu daga cikin bayanan dai sun kasance masu kunyata jam'iyyar.