Nigeria: Gwamnati ta kasa tallafawa manoma

Image caption Manoman sun ce rashin samun lamuni na bunkasa noma na kawo masu cikas.

A Najeriya, kananan manoma na cigaba da kokawa kan rashin sanun rancen kudade daga gwamnati domin bunkasa harkar noma, duk kuwa da cika sharuddan da suka yi.

Hakan ya faru ne duk da alkwarin da gwamnatoci a matakai daban-daban kan yi masu na basu rancen shekara da shekaru.

Manoman dai na cewa rashin samun lamuni na bunkasa noma, na kawo masu cikas matuka.

A halin yanzu dai Najeriya na wani sabon yunkurin wadata kanta da abinci, a maimakon shigo da galibin abincin daga kasashen waje da kasar ke yi.

Labarai masu alaka