An sace hakimi da talakawansa a Bauchi

Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Ana yawan sace mutane a baya-bayan nan a jihar Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a Najeriya, na cewa wasu 'yan bindiga da ba a tantance ko su waye ba, sun sace wani basarake da kuma kananan yara a karamar hukumar Toro.

Bayanai na cewa an sace hakimin gundumar Tama, Malam Adamu Yakubu ne a gidansa, da kuma wasu kananan yara biyu a gidan makotan hakimin ranar Asabar da misalin karfe biyu na dare.

Sakataren hakimin yankin Lame, Adamu Muhammad, ya tabbatar wa BBC cewa 'yan bindigar sun yi kuma harbe-harbe a yankin kafin su yi awon gaba da mutanen zuwa wani wuri da har kawo yanzu ba a tabbatar da ko ina ne ba.

Ba a tabbatar da makasudin sace basaraken da kuma talakawan nasa ba, amma bayanai na cewa 'yan bindigar sun bar lambar wayarsu da cewa a tuntube su, amma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu magana da su.

Kokarin da wakilin BBC ya yi na jin ta bakin rundunar 'yan sanda a jihar ta Bauchi dai ya ci tura kawo lokacin wallafa wannan rahoto.

A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar sace-sacen mutane ana garkuwa da su domin karbar kudin fansa a jihar Bauchi da ma wasu jihohi na Arewaci da Kudancin Najeriya.

Labarai masu alaka