Musulman Faransa sun halarci makokin Fada

Image caption Musulman kasar sun yi Allah-wadai da kisan

Fiye da Musulmai 100 ne suka halarci taron addu'o'i na zaman makokin wani fadan coci da wasu masu tayar da kayar baya suka kashe a Faransa.

An yi taron addu'o'in ne a cocin Rouen Cathedral, bayan kwana biyar da kashe fadan.

Coci-coci daban-daban na kasar ne suka gayyaci musulman wajen taron addu'o'in zaman makokin, domin su nuna rashin amincewarsu kan kisan, wanda ake tunanin masu ikirarin jihadi ne suka yi.

An kashe limamin kiristan ne mai suna Jacques Hamel, a lokacin da yake jagorantar ibada a cikin majami'ar, inda maharan suka yi masa yanakan rago.