'Yan Indiya na cikin tsanani a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto India in Jeddah
Image caption 'Yan ciranin Indiya 10,00 ne suka rasa aiki a Saudiyya

Gwamnatin Indiya ta ce tana samar da kayan abinci ga dumbin 'yan kasarta da ke cikin halin-ha'ula'i a Saudiyya.

Ofishin jakadancin Indiya da ke birnin Jidda ya kai ziyara sansanonin da 'yan ciranin kasar ke zaune inda aka rarraba musu kayan abinci da ba za su iya saya ba.

Ministan harkokin wajen Indiya Sushma Swaraj, ya ce fiye da 'yan cirani 10,000 ne suke cikin barazana saboda rasa ayyukansu da suka yi a Saudiyya da Kuwait.

Hakan ya faru ne sakamakon halin tabarbarwar tattalin arziki da kasashen suka shiga.

Labarai masu alaka