Ambaliyar ruwa ta halaka mutane a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jihohin Agadas da Tawa ne matsalar ambaliyar ruwa ta fi shafa.

A Jamhuriyar Niger, kimanin mutane 11 ne suka rasa ransu yayin da mutane kusan dubu 30 suka rasa muhallansu sanadiyyar ambaliyar ruwa tsakanin watan Yuni kawo yanzu.

Jihohin Agadas da Tawa su ne matsalar ta fi shafa.

Majalisar dinkin duniya ce ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a karshen mako.

Sai dai tuni gwamnatin Niger din ta ce tana daukar matakai game da al'amarin.

Labarai masu alaka