Dakarun Niger sun karbe iko da Damasak

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar fiye da 20 a Diffa

Dakarun tsaro na Nijar sun karbe iko da garin Damasak da ke bakin iyakar Najeriya da kasar daga hannun 'yan Boko Haram.

Wata sanarwa da hukumomin tsaron Nijar din suka fitar ta ce a karshen makon jiya ne dakarun suka karbe garin, bayan wani farmaki da suka kai.

Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun samu tallafin mayakan sama na rundunar hadin guiwa ta MNJTF wajen kai farmakin da ya kai ga kwace garin na Damasak.

Yayin da dakarun Najeriya suma suka danna ta bangaren kudu domin murkushe ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Farmakin dai wani bangare ne na matakan da kasashen yankin Chadi ke dauka domin ganin sun kakkabe mayakan Boko Haram da ke boye a yankunan gabar kogin Komadugu.

Labarai masu alaka