An harbo jirgin Rasha a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Rasha na goyon bayan Bashar al-Assad

Hukumomi a Rasha sun ce 'yan kasar biyar ne suka mutu a lokacin da 'yan tawaye suka harbo jirgin da suke ciki a kasar Syria.

An harbo jirgin mai saukar ungulu samfurin Mi-8 ne a yankin Idlib.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce uku daga cikin mutanen da ke cikin jirgin ma'aikatansa ne, yayin da biyu kuma jami'an tsaro ne.

Jirgin na kan hanyarsa ne ta komawa sansaninsa bayan ya kai kayan agaji birnin Aleppo wanda aka yi wa kawanya.

Babu tabbacin mutanen da suka harbo jirgin.

Wata gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye, cikinsu har da masu fafutikar jihadi ce ke rike da ikon yankin na Idlib.

An dai taba harbo wani jirgin na Rasha, wacce ta kaddamar da hare-hare kan 'yan tawaye a karshen watan Satumbar shekarar 2015, domin taimaka wa gwamnatin Syria.

Labarai masu alaka