An kama wani ɗan damfara ɗan Nigeria

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption 'Mike' ya damfari mutane miliyoyin dala

Rundunar 'yan sandan duniya ta ce ta kama wani dan Najeriya da ke shugabancin masu amfani da shafukan intanet wajen damfarar jama'a.

Rundunar ta ce ta kama mutumin, wanda ya damfari mutane kimanin $60m, a birnin Fatakwal da ke jihar Ribas ta kudu maso kudancin kasar.

Rundunar 'yan sandan ta bayar da misalin cewa mutumin, wanda ta ce sunansa 'Mike', ya damfari wani mutum $15.4m a baya bayan nan.

Za a tuhumi mutumin da laifukan yin kutse da hada baki da kuma satar kudi ta hanyar yaudara, a cewar rundunar 'yan sandan.

Rundunar ta kara da cewa, "Gungun 'yan damfarar da Mike ke jagoranta ya sace bayanan email na kasuwancin mutane da dama a duk fadin duniya, cikinsu har da 'yan kasar Australia, Canada, India, Malaysia, Romania, Afirka ta kudu, Thailand da Amurka."