Kasafi: Abdulmumini ya bayyana a gaban APC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tuni ne shugaba Muhammadu Buhari yarattaba hannu a kan kasafin da ake cece-kuce a kansa

Tsohon shugaban kwamitin kasafin kuɗin Majalisar Wakilan Najeriya Abdulmumini Jibrin ya bayyana a gaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar domin yi mata bayani kan zargin aringizo a kasafin kuɗin ƙasar.

Yanzu haka dan majalisar yana can yana ganawar sirri da shugabannin jam'iyyar a hedikwatarta da ke Abuja.

Jam'iyyar ta APC ta bukaci ɗan majalisar ya bayyana ne game da cacar-bakin da yake yi da shugabannin majalisar a kafofin yaɗa labarai, a kan zargin aringizo a kasafin kuɗin Najeriyar na bana.

Batun aringizon dai na ci gaba da janyo kace-nake a ƙasar, inda har wasu daga cikin 'yan majalisar suka yi kira da a yi bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar lamarin.

Tuni dai jami'an hukumar tattara bayanan sirri na DSS suka rufe wasu ofisoshi na kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Wakilan.

Rikici ya barke a majalisar wakilan Najeriyar ne sakamakon zargin da Abdulmumini Jibrin ya yi cewa shugaban majalisar da mukarrabansa sun yi yunkurin yin aringizon N30bn a kasafin kudin shekarar 2016.

Dan majalisar, wanda aka sauke daga shugabancin kwamitin da ke kula da kasafin kudin na majalisar, ya ce an sauke shi ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar da za ta bada rigar-kariya ga shugabannin majalisar wakilan da ta dattawa.

Mista Jibrin ya kara da cewa "Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu 40bn a cikin 100bn da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta Najeriya.

Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga mumakin shugaban kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa.

A baya dai, dan majalisar wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a jihar Kano, yana daya daga cikin na hannun damar shugaban majalisar.

Labarai masu alaka