Saudiyya ta sallami dubban Indiyawa

Hakkin mallakar hoto VEER SINGH
Image caption Leburorin kuma na bukatar visa domin ficewa daga ƙasar Saudiyyar

Ministan harkokin wajen ƙasar Indiya, V K Singh zai kai ziyara Saudi Arabia domin tallafawa dubban laburori Indiyawa da suka rasa aiki a Saudiyyan.

Indiyawan wadanda mafiya yawansu leburori ne a kamfanonin gine-gine sun rasa ayyukansu saboda koma-bayan da fannin ya fuskanta sakamakon faduwar farashin danyen mai .

Indiya ta yi alkawarin kwashe mutanenta tare da basu agajin abinci na gaggawa a wasu lokutan.

A ƙasar Kuwait ma lndiyawa da ke aikin leburanci na fuskantar irin wannan yanayi sai dai nasu bai kai na Saudiyya muni ba.

Labarai masu alaka