Jirgi ya yi saukar gaggawa a Dubai

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wani faifan bidiyo ya nuna yadda jirgin ya dura kuma hayaki ya turnuke sama

Wani jirgin saman kamfanin Emirates da ke ɗauke da fasinjoji ya yi saukar gaggawa a filin jiragen sama na Dubai.

Hukumomi sun ce an kwashe fasinjojin da ma'aikatan jirgin su 300 lafiya daga jirgin wanda ya taso daga Indiya.

Sai dai wani jami'in kashe gobara ya rasa ransa a lokacin da suke aikin kashe wutar da ta kama a jirgin.

An kuma dakatar da sauka da tashin jirage a filin jirgin saman na wani dan lokaci.

Filin jirgin saman na Dubai shi ne ya fi kowanne hada-hada a yankin Gabas ta Tsakiya.

Fasinjojin jirgin kirar Boeing 777 sun ce sun fahimci an samu matsala da giyar jirgin.

Labarai masu alaka