Kun san illar rashin bacci?

Za mu iya bijirewa duk wani abu da zai iya saka mu bacci na dan wani lokaci, to amma fa idan tafiya ta yi tafiya, rashin baccin na iya haifar da dan karamin tabin hankali - A wani lokaci ma har ya kai ga mutuwa. Kamar yadda Adam Hadhazy ya gano mana.

Kamar yadda Adam Hadhazy ya gano mana.

Mutane na fara wasu irin tunane-tunane har ma su iya fara wasu dabi'u da ke nuna sun samu motsuwa.

Akwai mamaki a kan yadda muke gudanar da rayuwar mu. Idan ka kai shekaru 78 a duniya, wani lisafi na cewa za ka shafe shekara tara kana kallon talabijin, za ka shafe shekara hudu kana tukin mota, kwanaki 92 kuma ka na ban ɗaki, sannan za ka shafe kwanaki 48 kana jima'i.

To sai dai idan ana maganar abubuwan da ke ɗaukar lokaci, to akwai abin da ya sha gaban duk waɗannan.

Idan ka kai shekaru 78, akalla za ka shafe shekara 25 kana bacci.

A wani kokaci na daidaita lokutan ka, zai yi kyau ka tambayi cewa, har tsawon wane lokaci ne za mu iya zama a farke? Kuma menene illar rashin bacci?

Erin Hanlon wata farfesa a cibiyar nazarin bacci a jami'ar Chicago ta ce "Dukkan lafiyayyen mutum zai iya gane cewa bukatar yin bacci ta kan zarta bukatar cin abinci. Kwakwalwar ka za ta fara bacci kawai duk kuwa irin yunkurin da ka yi na ka wartsakar da ita"

To in haka ne me ke sa mu bacci?

Har yanzu an kasa gano hakikanin abin da ke samu bacci. Har yanzu an gaza yin bayanin aikin da bacci ya ke yiwa jikin ɗan adam, kamar yadda farfesar ta faɗa. Sai dai ta kara da cewa akwai wani abu dangane da bacci da ya ke nuna cewa yana bawa abubuwan da ke aiki a jikin mu damar su huta.

Bincike ya nuna cewa yawan bacci da kuma yin sa a kai-a kai ya na sa saurin warkewa (idan aka ji rauni), yana kara garkuwar jiki, yana inganta karfin jiki. Sannan abin da ya fi komai shi ne mutum yana tashi a wartsake bayan ya yi isasshen bacci.

Hakkin mallakar hoto Getty

A bangare daya kuma rashin wadataccen bacci yana iya haifar da ciwon suga, da ciwon zuciya, da kiba fiye da kima, yana ma iya haifar da damuwa da kuma ciwon jiki.

Domin magance wadannan matsalolin, idan dare ya yi sai jikin mu ya yi rauni, mu kama jin rashin dadi, mu ringa fama da kasala, sai kuma mu ji idan mu ya yi nauyi, yana kokarin rufe wa. Idan kuma mu ka ci gaba da dage wa muna cewa ba za mu yi bacci ba, sai mu kasa yin duk wasu abubuwa da muke yi, daga nan sai mu fara manta abubuwa.

Idan mu ka yi watsi da dukkanin wadannan alamun na bacci, mu ka ki yin baccin har zuwa wasu 'yan kwanaki, kwakwalen mu za su iya shiga rudani, sai mu fara wasu mugayen tunane-tunane, sai mu ringa raya abubuwan da a zahiri ba bu su, A cewar Atul Malhotra daraktar sashin kula da bacci a jami'ar California.

Binikice da dama sun nuna yadda jikin mutum yake samun matsala sabo da rashin isasshen bacci, ya ke kuma shafar yadda jikin dan adam ke aiki, musamman ma yana haifar da matsala a ƙoda, da kuma shafar yadda jin ke gudana.

Hakkin mallakar hoto Getty

To sai dai fa duk wadannan matsalolin da da rashin bacci ke haifar wa, ba sa dawwama, suna kaucewa idan mutum ya samu isasshen bacci. Idan ma akwai illa da hakan ya haifar, ta na gushewa. A cewar Farfesa Jerome Siegel, na sashin nazarin bacci a jami'ar California.

To idan baccin bai zo ba fa?

Akwai wata cuta da ake gado mai suna Fatal Familial Insomnia a turance -wacce ba kasafaia ake samun masu dauke da ita ba- tana haifar da karancin bacci matuka ga duk wadan da ke dauke da cutar. To amma fa kimanin iyalai arba'in ne a fadin duniya kawai suke da gadon wannan cuta.

Farfesa Malhotra ya ce "Wasu kwayoyi ne suke haifar da wasu nau'ikan sinadarai da ke ƙara ƙarfin jini, sannan sai su rikide zuwa wata cuta, dan haka ba za su yi aikin su yadda ya kamta ba. Wannan cutar ita ce ke hana mutane bacci sai dai su kasance a farke ko yaushe"

Cutar dai wacce ake kira Prions a turance wacce ta ke shiga cikin jini, ta yi masa illa, sannan ta haifar da wasu hudoji a cikin kwakwalwa, kuma ta ke shafar bangaren kwakwalwa da ke kula da bacci.

Mutumin da ya ke da irin wannan cuta ya kan rasa hutu, sai kuma ya fara wasu dabi'u irin na yara.

Hakkin mallakar hoto g

Bayan 'yan makwannai sai mai dauke da cutar ya fara dab'iu irin na mutumin da yake cikin wata damuwa. Daga nan sai ya zama yana tafiya tamkar mai bacci, sai ya fara rama, daga nan sai ya fara zama wani shir-shiri, sai kuma mutuwa ta biyo baya.

To sai dai fa har yanzu ba a tabbatar da cewa ko rashin baccin shi ne ya ke janyo mutuwa ba, sabo gadon cutar rashin bacci ya na lalata kwakwalwa.

Masu wannan ra'ayi kamar Seigel na bada misali da cewa, ba a ga mutanen da aka tsare a gidan yari suna mutuwa ba sabo da an hana su bacci, duk kuwa da cewa suna shiga tsananin wahala.

Haka kuma binciken da aka gudanar a kan dabbobi ya nuna cewa rashin bacci ba shi ne dalilin da ke janyo mutuwa ba, sai dai illar da rashin baccin ya haifar ta iya kai wa ga rasa rai.

Allan Rechtschaffen ya gudanar da wani bincike a jami'ar Chicago cikin shekarun 1980 inda ya daura wasu beraye a kan wani faranti aka kuma daura su a kan ruwa. A duk lokacin da beran ya yi yunkurin bacci sai farantin ya karkata beran ruwa ya taba shi. Daga nan sai ya farka.

Hakkin mallakar hoto Getty

Gaba daya berayen sun mutu a cikin wata daya, to sai dai ba a tabbatar da dalilin mutuwar ta su ba. sai dai zai iya yiwuwa halin da suka shiga ne na kasncewa a farke tsawon wani lokaci

Siegel ya ce, akwai babbar matsala wajen yin bayanin bincike a kan dan adam da dabbobi. Ba yadda za a hana mutum bacci ba tare da san ran sa ba, sannan a ce ba zai shiga wata damuwa ba. Seigel ya ce idan har wanda abin ya shafa ya mutu abin tambaya shi ne shin rashin baccin ne ya kashe shi, ko kuma damuwa ce? Har yanzu babu tabbataccen banbanci.

Wadannan abubuwan dai sun sa mutane sun daina kokarin gano iya wa'adin da mutum zai daka ba tare da bacci ba. to sai dai har zuwa yaushe ne za mu iya kai a farke?

Bayanan da ake da su dai na tsawon lokacin da dan adama ya shafe a farke su ne na Randy Gardner, wani matashi mai shekaru 17 a birnin San Diego da ke jaihar California na Amurka.

To sai dai fa ya gaza kaiwa wa'adin da aka diba na shafe sa'o'i 264 ko kuma kwanaki 11 ba tare da ko da gyangyadawa ba.

Bayan labarin na Diego akwai kuma wasu bayanan da ba su kai na sa inganci ba, cikin su kuwa har da na wata 'yar Birntaniya wacce a 1977 ta lashe wata gasar rashin bacci har tsawon kwanaki 18.

To amma sabo da fahimtar illar rashin baccin, musamman ma gano cewa mutane na jefa kan su cikin hadari dan neman suna, ya sa littafin nan mai adana bayanan mutanen da suka fi fice wato kundin Guinness Book of Records ya dai na bibiyar mutane da suka fi dadewa ba su yi bacci ba tun bara.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilshi latsa nan. How long can we stay awake