Za ka auri matar da bata iya girki ba?

Wani fitaccen Malamin addinin Kirista a Najeriya, Fasto Enoch Adeboye, ya gargadi maza cewa kada su auri matar da bata iya girki ba.

A wani bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta da muhawara, Enoch Adeboye, ya gargadi masu shirin yin auren cewa "kada ku auri mace don kawai ta iya rera waka. Ku auri matar da ta iya addu'a. Idan mace ba za ta iya yi maka addu'a tsawon awa daya ba, kada ka aure ta."

Fasto Adeboye ya kara da cewa, "Kada ku auri macen da bata iya girki ba, dole ta san yadda ake girki kafin ka aure ta domin kuwa ba za ta bar ka da fita waje domin sayen abinci ba."

Wannan batu dai ya jawo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta na kasar, inda wasu ke yaba masa, yayin da wasu ke caccakarsa.

Labarai masu alaka