Boko Haram ta rabu gida biyu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shekau ya ce ba zai daina fafutikar kafa daular Musulinci ba

Tsohon Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi watsi da matakin maye gurbin sa da kungiyar masu fafutukar kafa daular Musulunci a Iraqi da Syria wato IS ta yi da wanin sa.

A ranar Laraba ne aka nada Abu Mus'ab Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar IS reshen yammacin Afirka.

Amma Abubakar Shekau wanda aka shafe shekara guda ba ji duriyar sa da ta sauran magoya bayan sa ba, ya bayyana sabon shugaban da cewa kafiri ne da ya kaucewa tafarkin da kungiyar Boko Haram ke kai.

Ya kuma jaddada ce wa shi da magoya bayan sa su na nan kan akidar su:

Sharhi - Nasidi Adamu Yahya, Abuja

Masu sharhi a kan harkokin tsaro na ganin wannan sa-toka-sa-katsi tsakanin shugabannin Boko Haram wata babbar alama ce da ke nuna cewa an samu gagarumar baraka tsakanin manyan kungiyar ta Boko Haram.

A baya dai Abubakar Shekau ya ce sun yi mubaya'a ga IS, don haka nadin da kungiyar ta yi wa Abu Mus'ab Al-Barnawi wata mahangurba ce a gare shi.

Kazalika, hakan zai sake bai wa jami'an tsaro damar murkushe gyauron 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram, wadanda a yanzu kawunansu suka rabu.

Labarai masu alaka