Iran ta rataye 'yan Sunna 20

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumomi a kasar Iran sun rataye fursunoni 20 mabiya mazahabin Sunna, wadanda aka ce sun kai wani hari.

Kafofin watsa labarai na kasar sun ce an rataye mutanen ne ranar Talata saboda kisan wasu mata da yara da suka yi tsakanin shekarar 2009 da 2011.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce kasar ta Iran, wacce akasarin mazaunanta 'yan Shia ne, ta kashe akalla mutum 977 a shekarar da ta gabata.

Amnesty International ta soki hukumomin kasar kan kisan na baya bayan nan, tana mai cewa babu adalci a shari'ar da aka yi wa mutanen.