Kwakwalwar masu kiba na rauni cikin sauri

Masu taiba
Image caption Masu taiba

Wani bincike a Burtaniya ya nuna cewa bayan cika shekaru arba'in, kwakwalen mutanen da ke da kiba ko taiba na yin rauni cikin sauri, fiye da siraran mutane.

Masana kimiyya a Jami'ar Cambridge sun gano cewa kwakwalen masu taibar ta nuna karancin wani farin abu dake aikewa da sakonni tsakanin sassa daban-daban na kwakwalwa, dake kama da na siraran mutanen da suka dara su da shekaru goma.

Masanan sun yi gwaji a kan wasu mutane dari biyar, inda suka gano sauye-sauyen sun bayyana ne a tsakanin matsakaitan mutane.

Sun ce babu tabbaci kan ko kibar ce ke haddasa sauye-sauyen, ko kuma karancin wannan farin abu dake jikin kwakwalwar ne ke kara haifar da kibar.

Amma kuma sun ce yana da matukar muhimmanci a fadada binciken, saboda yanayin yadda ake samun karuwar masu kiba ko taiba a Burtaniya.

Labarai masu alaka