Apple zai sayar da makamashin da ya samar daga hasken rana

Hakkin mallakar hoto Getty

An amincewa katafaren kamfanin nan na Apple sayar da makamashin da ya samar daga hasken rana akan kudi $850 a California.

A shekarar data gabata, kamfanin ya samar da Acre power 2,900 wadda za a iya samar da hasken wutar da ya kai megawatts 130.

Yanzu haka an bawa Apple damar sayar da makamashin a kasuwanni.

Kamfanin ya ce makamashin da ya samar zai iya bayar da hasken wutar lantarki ga gidaje dubu sittin a California.

Wani kwararre ya ce wutar lantarkin da aka samar ta hanyar hasken rana bata da tabbas.

Dr Niall Mac Dowell, wanda malami ne a kwalejin Imperial da ke Landan, ya shaidawa BBC cewa, dan kamfanin Apple ya samar da makamashi ta hanyar hasken rana, ba lallai ba ne ya yi dai-dai da sauran makashin da ake samarwa ta wasu hanyoyin na daban ba.