Za a bude gasar Olympics a Rio

Olympics
Image caption Yau za a bude gasar a hukumace.

Shugaban riko na kasar Brazil Michel Temer, ya ce ya na da kwarin gwiwar 'yan kasar za su yi farin ciki idan aka fara gasar wasannin Olympic a yau juma'a.

Mista Temer ya ce karbar bakuncin gasar da Brzil ta yi, duk kuwa da matsin tattalin arziki da rikicin siyasa da kasar ke ciki, ya nuna cewa za ta iya shawo kan matsalolinta.

Kwamitin wasannin Olymics na kasar Rasha, ya ce an gama tantance 'yan wasa 271 daga cikin 387 da za su halarci wasan, yayin da wasu biyar ke jiran a yanke hukunci na karshe.

Shugaban kwamitin Alexander Zhukov ya ce Rasha za ta samu 'yan wasan da suka fi kowanne a gasar ta bana.

Tun da fari jagoran kwamitin gasar Olympics Thomas Batc ya sanar da cewa a wannan karon masu shan kwayoyi ba za su taba sakata su wala ba, dan duk inda suke gwajin da za a gudanar a wurin zai fallasa su.

Labarai masu alaka