ZTE ya baiwa jama'a damar fasalta wayar salula

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin wayar salula na ZTE ya bukaci jama'a su tallafa wajen samar da fasalin sabuwar wayar salula da zasu ƙera nan gaba.

Kamfanin ZTE na China ya kaddamar da wani shafin Internet inda jama'a zasu shiga domin gabatar da fasalin sabuwar wayar salula da suke son kamfanin ya ƙera.

Kuma jama'a zasu zabi fasalin da suka fi so ya ƙera.

Daga cikin waɗanda aka gabatar ya zuwa yanzu, akwai wanda yake son a ƙera waya wadda gidanta zai kasance na na'urar samar da makamashi daga hasken rana.

Kamfanin ZTE ya yi alƙawarin bayyana fasalin wayar salula da ya amince da zai ƙera baɗi.

ZTE kamfanin wayar salula ne na China da ya soma karbar shawara akan irin wayar da ya kamata ya ƙera daga ranar 3 ga wannan watan.