Saudiya za ta taimaki Jamus gano mahara

Rahotanni sun ce Saudiya ta yi tayin taimakawa Jamus gano 'yan bindigan da ake gani su suka kai hare-hare a Jamus a watan jiya.

Mujallar Der Spiegel ta tsinkayi wasu manyan jami'an Saudiya na cewa kasashen biyu za su yi duk kan mai yiwuwa don gano irin rawar da 'yan kasar Saudiyan suka taka a hare-haren.

Akwai rahotannin da ke cewa duk kan maharan biyu sun yi mu'amala da mayakan kungiyar IS, wadanda suka cusa musu tsatssaurar akida da basu umurni.

An ce daya daga cikin mayakan IS din da aka yi mu'amala da su, dan kasar Saudiya ne.

Daya daga cikin maharan ya yi hakkon fasinjojin jirgin kasa ne, yayin da dayan ya kai hari wajen wata dabdala.

Mutane da dama ne suka jikkata a hare-haren, yayainda aka kashe maharan kuma.

Labarai masu alaka