South Africa: Jam'iyyar ANC ta sha kayi

Hakkin mallakar hoto

Sakamakon karshe na larduna a Afrika ta Kudu ya tabbatar da cewa, jam'iyya mai mulkin kasar ta ANC ta sha kayin da bata gani ba tun da ta kafa gwamnati a karshen mulkin nuna wariya.

Jam'iyyar ta ANC ta yi rawar gani a birnin Johannesburg, sai dai kuma jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ta samu nasara a manyan birane da suke hada da babban birnin kasar Pretoria da Port Elizabeth.

Shugaban kasar acob Zuma, ya yi karfin hali wajen bayyana cewa dimokradiyyar kasar ta na kara karfe duk da kayin da jam'iiyarsa ta sha.

Labarai masu alaka