Thailand: Ana zaɓen raba gardama

Hakkin mallakar hoto AFP

Jama'a a Thailand na kaɗa ƙuri'a a wani zaɓen raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar da zai baiwa sojoji damar ci gaba da mulki.

Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama dai sun soki yadda sojoji suka shirya zaben na raba gardama, saboda an hana yakkn neman zaɓe, lamarin da sanadiyyarsa aka kama mutane da dama.

Saboda haka nema jama'a basu da cikakkiyar fahimtar daftarin kundin tsarin mulkin.

'Yan ƙasar Thailand da dama sun ce, basu ma san abinda kundin tsarin mulkin ya kunsa ba.

Idan har gwamnatin mulkin soja ta amince da kundin tsarin mulkin za a yi zaɓe a ƙarshen baɗi, domin maida kasar bisa turbar dimukradiyya.

Amma masu suka sun ce, daftarin kundin tsarin mulkin zai haifar da dimukradiyya mai rauni

Cikin shekara ta 2014 ne sojoji suka yi fatali da tsohon kundin tsarin mulkin kasar bayan sun yi juyin mulki

Kafin nan dai sai da kasar ta auka cikin rudani a siyasance.

Labarai masu alaka