Kashe sojoji: An kama mutane 57 a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar sojin Najeriya ta ce an kashe wasu sojojinta 11 yayin da aka raunata biyu a kwantan baunar da wasu 'yan bindiga suka yiwa sojojin kasar a jihar Neja.

A wata sanarwa, rundunar ta ce wani sojinta guda ya bace, sai dai dakarunta sun kashe 'yan bindiga 8 tare da cafke wasu mutum 57.

Sanarwar ta kara da cewa sojin Najeriyar sun kuma kwace wasu manyan makamai daga hannun 'yan bindigar.

Lamarin dai ya auku ne lokacin da sojojin ke kan hanyar su ta zuwa fatattakar 'yan bindigar a maboyar su a kauyukan Kopa da Dagma da kuma kauyen Gagaw dake karamar hukumar Bosso a jihar.

Kanar Sani Usman Kuka sheka , shi ne kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, ya kuma yi wa Aisha Shariff Baffa karin bayani ga abinda ya ke cewa;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka