An kashe masu zanga zanga a Habasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gudanar da gagarumin zanga zanga a yankin Oromia da ke kusa Addis Ababa babban birnin kasar

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an kashe mutane da dama a lokacin da su ke zanga zangar kin jinin gwamnati a garin Bahir Dar da ke arewa maso yammacin kasar Habasha.

Wani mutum da ya ga lamarin ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaro sun harbi abokinsa aka.

Kakakin gwamnatin yankin Amhara ya ce masu zanga a Bahir Dar sun lalata kayayyaki, inda suka yi yunkurin kafa tsohuwar tutar kasar a ofisoshin gwamnati.

An kuma gudanar da gagarumar zanga zanga a yankin Oromia da ke kusa da Addis Ababa, babban birnin kasar.

Gwamnatin Habasha dai ta bayyana zanga zangar da manyan kabilu biyu na kasar su ka gudanar a matsayin haramtacciya.

Labarai masu alaka