Masu fito na 'tsaka-mai-wuya' a Nigeria

Shugaba Buhari
Image caption Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin sanya ido a shige da ficen kaya ta gabar tekun kasar.

Kungiyar masu fiton kaya daga kasashen ketare zuwa Najeriya sun ce akwai yiwuwar mutum kusan miliyan uku ne da ke cin abinci ta wannan hanyar su rasa ayyukansu.

Kungiyar ta ce karin kashi 43 cikin 100 na haraji ko kuma kudin fito da hukumar kwastam ta yi da kuma hauhawar farashin dala sun sa da yawa daga wadanda ke gudanar da harkokinsu sun daina.

Dillalan da ke fiton kayan a gabar tekun Najeriya sun ce yawanci sun ajiye aikin nasu ne sakamakon halin da suka tsinci kan su a ciki, tun bayan karin kudin futon.

Sun kara da cewa tuni wasu daga cikin su suka yi kaura zuwa kasashe makwabta.

Kwararru dai na ganin cewa halin da ake ciki ya janyo jiragen dakon kaya sun rage zuwa Najeriya, yayin da mutane da dama suka rasa ayyukan yi.

Labarai masu alaka