Buhari ya rantsar da masu ba shi shawara

Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari, ya rantsar da wasu sabbin masu ba shi shawara na musamman a ranar Laraba.

Wadanda aka rantsar sun hada da Dokta Adeyemi Dipeolu a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman a kan al'amuran tattalin arziki, da Alhaji Tijjani Abdullahi, wanda aka bai wa muƙamin mai ba da shawara na musamman a kan tsare-tsare.

Barrista Maryam Uwais kuma ita ce mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman a kan raya al'umma.

Yayin da Sanata Babafemi Ojodu ya zama mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman a bangaren sha'anin siyasa.

An dai daɗe ana ƙorafi a kan cewa Shugaba Buhari ba shi da masu ba shi shawara a kan wasu muhimman al'amura, abin da ake ganin yana jawo tsaiko wajen tafiyar da ayyukan da shugaban ƙasar ke gudanarwa.

Labarai masu alaka