Kasafin kudi: 'Ba ma tsoron binciken EFCC'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugabannin majalisar wakilan Najeriya sun ce ba sa wata fargabar binciken da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati za ta yi a kan zargin yin cushe a kasafin kudinshekarar 2016.

Mai tsawatarwa na majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya shaida wa BBC ya ce ba su ci nanin ba don haka nanin ba za ta ci su ba.

A cewarsa doka ce ta kafa hukumar EFCC, don tana da ikon gudanar da binciken, yana mai cewa a shirye yake ya amsa dukkan tambayoyin da za a yi masa game da kasafin kudin.

Sai dai ya musanta cewa sun yi cushen kudade a kasafin kudin na bana, kamar yadda tsohon shugaban kwamitin kasafin kudin Abdulmumini Jibrin ke zargin su da aikatawa.

Shi dai Jibrin ya zargi shugaban majalisar Yakubu Dogara da Alhassan Ado Doguwa da wasu manyan 'yan majalisar da yunkurin yin cushen sama da N70bn a kasafin kudin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka