Ana zabe a kasar Zambia

'Yan sandan Zambia a wurin zabe
Image caption Shugaba Edgar Lungu na neman yin tazarce.

'Yan kasar Zambia sun fara jefa kuri'a a zaben shugaban kasar da ake yi ranar Alhamis.

'Yan takara tara ne dai suka fito neman kujerar, sai dai ana ganin fafatawa za ta fi yin zafi ne tsakanin Shugaba Edgar Lungu da fitaccen dan kasuwar nan Hakainde Hichilema.

A karon farko wanda ya lashe zaben dole ne ya samu kuri'u da gagarumin rinjaye, idan ba haka ba sai an je zagaye na biyu.

Al'ummar kasar sun fito kwansu da kwarkwatarsu a babban birnin kasar, Lusaka, cike da doki saboda ana sa ran miliyoyin su za su kada kuri'a a safiyar nan.

Shugaba Edgar Lungu na neman yin ta-zarce, bayan ya gaji mulki a hannun marigayi Shugaba Micheal Sata, ya kuma yi nasara ne bayan zaben da aka yi a watan Oktobar shekarar 2014.

Tattalin arzikin Zambia ya fada mawuyacin hali, saboda karyewar farashin Copper da ke samarwa kasar kudaden shiga daga kasashen waje.

Labarai masu alaka