Ana gwabza fada a wajen birnin Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rahotanni sun ce an kashe akalla mutane talatin a Raqqa tungar 'yan kungiyar IS

Ƙazamin faɗa ya ɓarke a wajen birnin Aleppo da ke kudu-maso-yammacin Syria, bayan an kawo ƙarshen tsagaita wuta na sa'oi uku da Rasha ta sanar.

Masu fafutuka sun ce sun ga an kai farmaki da dama da jiragen yaƙi da kuma jirage masu saukar ungulu.

Yayin da wasu rahotanni ke cewa an cigaba da ɓarin wuta a wuraren da 'yan tawaye ke rike da su.

Ana gwabza faɗan ne a gundumar Ramouseh, inda 'yan tawaye suka samu balle ƙawanyar da dakarun gwamnati suka yi wa birnin, wanda aka raba ikonsa tsakanin 'yan tawayen da kuma gwamnati.

Rasha dai ta sanar da tsagaita wutar ne domin bayar da damar shigar da kayan agaji yankin.

Labarai masu alaka