'Yar London da ta shiga IS 'ta mutu'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amira Abase da Kadiza Sultana da kuma shamima Begum sun shiga jirgi zuwa Turkiyya sannan suka wuce Syria

An yi amanna cewa ɗaya daga cikin 'yan mata uku 'yan makaranta da suka bar London domin shiga ƙungiyar masu ikirarin kafa daular musulunci ta IS ta mutu.

Kadiza Sultana da sauran 'yan matan sun bar kudancin London a bara zuwa Syria domin shiga kungiyar, amma lauyan da ke wakiltan iyalan Kadiza, Tasnime Akunjee ya shaida wa BBC cewa sun samu labarin cewa ta mutu a wani farmaki da Rasha ta kai ta sama a birnin Raqqa.

Sai dai ya ce basu iya tabbatar da haka ta wata kafa mai zaman kanta ba, saboda yanayin da ake ciki a Syria.

Inda ya ƙara da cewa Kadiza wadda ta bar London tana da shekaru 16 da fahimci halin da ake ciki kuma ta yi ƙoƙarin barin ƙungiyar ta IS ta komo gida, amma ta ji tsoron kada 'yan kungiyar su kama ta su hukunta ta.

Lauyan ya ce iyalan Kadiza sun kaɗu matuka da labarin mutuwarta.

Labarai masu alaka