Lungu ya sake lashe zabe a Zambia

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jam'iyyar PTF mai mulki ta musanta zargin magudin

Hukumar zabe ta Zambia ta sanar da cewa shugaban kasar mai ci yanzu, Edgar Lungu ne ya sake lashe babban zaben da aka yi.

Hukumar zaben ta ce mista Lungu ya samu fiye da kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka kada a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yayin da babban abokin hamayyarsa, Hakainde Hichilema ya samu fiye da kashi 47 cikin dari.

Tun da fari babbar jam'iyyar adawa ta UPND ta yi zargin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasar.

Inda ta yi kira da a sake kidaya kuri'u a babban birnin kasar wato Lusaka .

Labarai masu alaka