'Za mu dauki mataki kan kisan 'yan shi'a'

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce za a dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka samu da aikata laifi a rikicin da ya faru tsakanin 'yan shia da sojojin kasar a garin zaria cikin watan disambar bara.

Wata sanarwa da mai taimakawa shugaban na Nigeiria kan kafafen yada labarai, Garba Shehu, ya fitar ta ce shugaba Buhari yana nazari kan rahoton da kwamitin bincike ya mikawa gwamnantin Kaduna kan rikicin.

Ya ce masu fafutukar kare hakkin bil adama na gida da kuma na waje su kwantar da hankalinsu, domin kuwa duk wanda aka samu da laifi zai yabawa aya zakinta.

A lokacin wata tattaunawa da shugaba Buhari ya yi da manema labarai a baya, shugaban ya ce yana jiran rahoton kwamitin binciken, kafin ya dauki matakin da ya dace.

Labarai masu alaka