'Yan gudun hijirar na wahala a Girka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yan gudun hijirar Girka

Kungiyar agaji ta Save The Children ta kasar Burtaniya, ta yi gargadi game tabbarbarewar halin rayuwar da 'yan gudun hijira a tsiburan kasar Girka suke ciki.

Rayuwa na kara tsananta ne ga 'yan gudun hijirar, sabo da yawansu da ke karuwa bila-addadan.

Kwararowar da 'yan gudun hijirar suka yi zuwa tsiburan Lesbos da Chio da kuma Samos na kasar Girkar, a cikin rabin farkon wannan wata, ya karu da kusan kashi 150 cikin 100, idan aka danganta da yawan wadanda suka shigo a rabin farko na watan Yuly.

Kungiyar Agajin ta Save The Children, ta furta cewa 'yan gudun hijirar da ke shigowa a wadannan yankuna na fuskantar kangi da dama,musamman game da abun da ya shafi abubuwa kamar wuraren wanka da na ba haya da kuma ruwan sha.

Sun kasance cikin wanni irin yanayi na rashin ruwan sha da na shayi.

Save The Children na son kungiyar tarrayar turai ta bunkasa abubuwan more rayuwa ga mutanan tare da gaggauta soma gudanar da tsarinan na tsugunnar da 'yan gudun hijira na gangariya a cikin sauren kasashe mambobi kamar yadda aka tsara tun a baya.

Labarai masu alaka