An saki fursunoni dubu 38 a Turkiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fursunoni dubu 38 ne suka ci moriyar afuwar

Gwamnatin Turkiya ta ce za ta saki mutane dubu 38 dake zaman gidan kaso a wani mataki na gyara halin ka.

Duka wadanda za a saki ɗin dai waɗanda aka yankewa hukunci ne gabanin yunƙurin juyin mulki a watan jiya.

To sai dai daga cikin mutanen da aka yi wa afuwar ban da waɗanda aka yankewa hukunci sabo da laifukan kisan kai da fyade da kuma ta'addanci.

Gwamnati dai ba ta bada dalilin yin afuwar ba, to amma wasu na ganin mai yuwawa gwamnatin ta yi haka ne domin ta samu sararin da za ta kulle dubban mutanen da aka kama bayan yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasar ba.

Haka kuma gwamnatin ta kafa wata doka da a ƙarƙashinta aka kori sama da 'yan sanda dubu biyu da kuma ɗaruruwan sojoji bisa zarginsu da hannu a yunƙurin juyin mulkin.

An kuma kori jami'ai da dama daga kamfanin sadarwa na ƙasar.

Labarai masu alaka