Tasirin finafinai wurin tuna shugabannin kasa

Wasu finafinan da aka yi akan shugabannin kasar Amurka na girmamawa ne, kamar guda biyun da ke shirin fitowa game da Barack Obama. Amma wadansu da dama kishiryar hakan ne.

Finafinai sun yi tasiri kan yadda mu ke tuna shugabannin kasar Amurka tun daga Lincoln zuwa ga JF Kennedy. Yayin da ake shirin fitar da finafinai biyu game da shugaba Obama, ko su ma za su yi tasiri kan tarihinsa?

Shugabannin kasa na bukatar cika wasu sharuda kafin a yi fim din su: Wajibi shugaban ya zama ya na da kwarjini da muhibba. “Masana’antar Hollywood na son nuna yadda ake daukar muhimman matakai, tare da furta muhimman bayanai,” in ji Iwan Morgan, farfesan nazarin al’amuran Amurka a jami’ar University College London.

Don haka fasahar zancen shugaba Obama za ta iya ba shi damar shiga cikin wannan rukuni, sai dai kuma wasu masanan na ganin za a fuskanci kalubale wurin yin fim din Obama.

“Sai mun tabbatar da cewa akwai wani ginshikin labari bayan batun launin fatarsa,” in ji Toby Miller, farfesa mai ritaya a fannin kafafen yada labarai da al’ada na jami’ar California. “Labarin Clinton shi ne neman mata, Kennedy kuma abin tausayi, shi kuma Nixon abin kunya. To me ye labarin Obama in ka dauke cewa shi bakar fata ne?”

Hakkin mallakar hoto White house

Ana ganin cewa wa’adin zangon mulki biyu da Obama ya kwashe a fadar White House babu wani abin tashin hankali ko abin mamaki da zai iya kayatar da masu kallon finafinai.

“Babu wasu gagarumin shirye-shirye da ya yi wadanda za a yi bada labarinsu a sigar fim. Ta yaya za kai fim a kan Obamacare? Ina hasashen cewa fim din da za a yi a kan Obama zai fi mai da hankali ne kan waye shi maimakon abinda ya aikata,” in ji Farfesa Morgan.

Ba mamaki wannan ce ta sa finafinan Obama guda biyu da ke shirin fita kasuwa su ka mai da hankali ga zamanin kuruciyarsa tun ma bai shiga siyasa ba. Southside with You, wand zai fito a watan Agusta a Amurka, na kunshe ne da labarin yini daya a Chicago, wato ranar da Baraka Obama ya fara fita zance da matarsa.

“Ina ganin a lokacin ya fara sunsunar cewa zai iya taka rawa a siyasa amma bai tantance ko ta wacce hanya ba. Ba na ganinsa a matsayim fim din da ya shafi siyasa. Soyayya ce zalla,” in ji Parker Sawyers, dan wasan da ya fito a matsayin Barack a fim din.

Hakkin mallakar hoto Roadside Attraction

Daya fim din mai suna Baryy, kuma an gina labarinsa ne a New York a shekaran 1981 a lokacin shugaban kasar ya na dalibin jami’a. Sai dai babu cikakken bayani kawo yanzu game da labarin fim din in ban da cewa matashi Obama ya hadu da wata budurwa.

Wadannan finafinan farko da aka shirya a kan Obama, duk da cewa ana ta marmarin fitowarsu ba za su yi wani tasiri kan tarihinsa ba, kasancewar babu taurarin ‘yan wasa a ciki da za su ja hankalin masu kallo.

“Finafinan za su iya tasiri, amma ka tuna mutane nawa ne za su kalle su? Mutanen da ba sa son Obama ba za su je kallon labarin soyayyarsa da Michelle ba,” in ji Joseph Uscinski, mataimakin farfesan nazarin siyasa a jami’ar Miami.

Finafinan da za su fi tasiri su ne wanda manyan kamfanoni za su narka dimbin kudi su yi labarin zamanin shugabancinsa. Yanzu haka manyan kamfanonin Hollywood na nazari kan labarin da su ka danganci shugabancin Obama, kuma littattafan da ya rubuta da kansa za su taimaka musu.

“Littafin da zai rubuta na bayanin shugabancinsa zai taimakawa Hollywood wurin samun gabar da za su gina labarin fim a kai.” Baya ga fim din Zero Dark Thirty na Kathryn Bigelow “matakin da ya dauka na kashe Bin Laden zai iya zama fin din Hollywood a nan gaba,” in ji Farfesa Morgan.

Hakkin mallakar hoto Longsgate

Hakika Obama zai dade kafin ya kamo abokan burminsa irin su Lincoln, wanda kawo yanzu an yi finafinai sun fi 40 a game da shi. Ana yawan yin labarin Lincoln, wanda a 2012 Steven Spielberg ya sake bada shi a fim din ‘Lincoln’ saboda ya dace da tsarin finafinan Hollywood. “Kakkarfan shugaban kasa ne da ke adawa da bauta kuma ya halarci yaki domin kawo karshenta,” in ji Uscinski.

A gaida shugaba

Nixon da JFK su ne fitattun shugabannin kasar da ake ganin fim ya yi matukar tasiri kan yadda ake tuna su. Fim din ‘All the President’s Men’ da ya nuna badkalar Watergate, ya sauya yadda mutane ke kallon Nixon har zuwa yau. “Fim din ya taimaka wurin nuna Nixon a matsayin wani mai kulle-kulle tare da kwarewa a kan munafurcin siyasa,” in ji Farfesa Morgan.

Sai dai kuma finafinai na iya nuna shugaban kasa ta fuskar da ba ta dace da gaskiya ba. Finafinai guda biyu, ‘Nixon’ na Oliver Stone, 1995 da ‘Frost/Nixon’ na Ron Howard, 2008 sun nuna rayuwar shugaban da ya sauka daga mukaminsa a matsayin abin tausayi. Farfesa Toby Miller ya ce wadannan finafinan “sun yi kokarin wanke sunansa.”

Hakika fim ya taka muhimmiyar rawa, wurin samar wa da masu kallo mahangar da za su rika tuna Kennedy, wanda a matsayinsa na shugaban kasa ya aikata muhimman abubuwa kafin a kashe shi a kan mulki.

Joseph Uscinski ya ce: “In da za ka tambayi mutane da yawa mai su ka sani game da JFK za su yi bayanin kashe shi da kuma wadanda su ka kitsa kisan. Saboda me? Saboda fim din Oliver Stone mai suna ‘JFK’.”

Hakkin mallakar hoto Dreamworks

Sai dai babu wata muhimmiyar rawa da finafinai su ka taka a tarihin shugabannin da ake kallo a matsayin kyanwar-lami ko mara sa hauragiya. Ga wasu mutanen, shugaba Dwight D Eisenhower, Ford, da Jimmy Carter na cikin wannan rukuni. “Ba gwaraza ba ne” in ji Farfesa Morgan. “Eisenhower na daya daga cikin shugabannin da suka fi kwazon aiki.

Ina ga mutane da yawa za su iya sa shi cikin jerin shugabanni 10 da suka fi kawo ci gaba a Amurka. Amma tsarin shugabancinsa babu bugun kirji ko tallata kai. Don haka Hollywood ba za ta samu abin nunawa ba.”

Shi kuwa shugaba Carter, abubuwan da yayi bayan barin fadar White House su ne za su iya daukar hankalin masu shirya finafinan Hollywood. “Tasirin Carter shi ne ya zamo wani muhimmin mutum bayan kammala shugabancin Amurka.

Don haka tarihin ya ta’allaka ne da shekaru 35 din da su ka biyo bayan saukarsa ba wai shekaru hudun da yayi a fadar White House ba. Ina kyautata zaton za a shirya fim akan haka a Hollywood,” in ji Farfesa Miller.

Ba finafinan Hollywood ne kadai ke da tasiri kan tarihin shugabanni ba, har ma shirye-shiryen talabijin masu nuna gaskiya tsurarta, sai dai su ba su cika sauya tunaninmu ba illa dai su tabbatar mana da kallon da mu ke musu.

Lokacin da Michael Moore ya gabatar da shirin Fahrenheit 9/11 ya samar da kakkausar suka ga shirin “Yaki da Ta’addanci” na shugaba George W Bush.

Sai dai babu wani cikakken tasiri da ya yi kan yadda al’umma ke tuna shugaba Bush. Abinda ya sa hakan kuwa saboda masu adawa da Bush ne kawai su ka kalli shirin.

Hakkin mallakar hoto Dreamwork

Bambancin ra’ayi ya taka muhimmiyar rawa kan yadda al’umma ke kallon shugabacin Obama. Hakan zai rage karfin tasirin finafinai akan tarihinsa. “Ba na jin da akwai sauran abinda fim zai iya yi game da yadda za a tuna Obama nan da shekaru 10 masu zuwa saboda tun ran gini run ran zane; Bakake na sonsa, ‘yan jam’iyyar Democrat na sonsa kwarai, ‘yan Republican na matukar kinsa,” in ji Joseph Uscinski.

Bugu da kari, Obama ba ritaya zai yi daga harkokin jama’a ba. Har yanzu da sauran kwarinsa. Zai iya yiwuwa ya ci gaba da yin abubuwan da za’a rika yada wa a kafafen yada labarai, abinda zai sa shi da kansa ya samu tasiri wurin bada tarihinsa.

Don haka zai yi wuya ga wani fim din Hollywood komai tsadarsa kuma komai shaharar taurarinsa ya yi wata rawar gani game da yadda za’a tuna shugaba Obama – akalla dai nan da ‘yan shekaru kadan.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How the movies shapes a president.