Iraqi: An rataye 'yan IS kan kisan 'yan Shi'a

Image caption Sojojin Shi'a da IS ta kashe

Ƙasar Iraqi ta zartar wa 'yan kungiyar IS guda 36 hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin kisan gilla ga kuratan sojojin fiye da 1,700, a tsohon sansanin sojin Amurka.

Ƙungiyar IS ta yi kai hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar sojojin, a sansanin soji na Camp Speicher da ke kusa da Tikrit, a 2014, lokacin da 'yan kungiyar suka karbe iko da arewacin Iraqi.

Mafi yawancin sojojin da IS din ta kashe mabiya mazhabar Shi'a ne.

Mayakan IS sun saki wasu hotunan bidiyo da kuma marasa motsi da ke nuna yadda aka kitsa kisan gillar da aka yi wa sojojin a 2014.

Daga baya ne kuma aka samu manyan ramukan da aka binne sojojin da aka kashe.

Image caption Ramukan da IS ta binne sojoji 'yan Shi'a

Kungiyar IS, mai ikrarin bin mazhabar Sunna, ta sha bayyana mabiya mazhabar Shi'a da 'yan bidi'a wadanda kuma ba musulmi ba.

Wannan ne ya sanya kungiyar tsaurara hare-hare kan mabiya mazhabar ta Shi'a.

Hakan ne ma ya sa aka samu shigar mayakan sa-kai na Shi'a wajen fafatawa da ganin an kawo karshen kungiyar ta IS.