Niger Delta Avengers ta yarda a yi sulhu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan bindigan yankin Niger Delta a Najeriya

Kungiyar 'yan bindiga ta Niger Delta Avenger a Najeriya ta ce za ta mutunta kiraye-kirayen da ake mata na dakatar da kai hare-hare a kudu maso gabashin kasar mai arzikin mai.

A ranar Juma'a, wasu dattijan yankin sun bukaci kungiyar da ta kawo karshen hare-haren da take kai wa, domin ba su sararin fara tattaunawa da gwamnatin Najeriya akan a karawa yankin kudade da ake samu daga mai.

Kungiyar ta Niger Delta Avengers ta ce ta yi maraba da wannan tayi, sai dai duk da haka kuma, an ci gaba da kai hare hare a kan na'urorin kamfanonin mai a yankin.

Wata sabuwar kungiya a yankin, mai suna Niger Delta Greenland Justice Mandate ta ce ta fasa wani bututun mai a jiya Asabar.

Wasu 'yan bindiga a yankin, sun ce suma za su ci gaba da gwagwarmayar da suke yi da makamai.

Hare-haren da 'yan bidiga a yankin suke kai wa kan kamfanonin mai sun janyo raguwar adadin mai da Najeriya ke samar wa.

Labarai masu alaka