An soki gwamnatin Bauchi kan cire sarakuna

Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar

A jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, ana ci gaba da cece-kuce dangane da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sauke wasu sarakunan gargajiya kimanin 1100 a fadin jihar.

Wasu mutane a jihar na ganin gwamnatin jihar ta sanya siyasa ne cikin batun, ganin cewa gwamnatin da ta shude ta PDP ce ta kirkiro karin masarautun.

Gwamnatin Barista, Muhammad Abdullahi Abubakar ta sauke hakimai da dagatai wadanda ta ce an nada su ba bisa ka'ida ba.

An dai kirkiro karin masarautun ne daga 2014 zuwa 2015 karkashin wata doka ta majalisa.

Sai dai wasu cikin wadanda aka sauke sun ce kawo yanzu ba su samu wata takarda daga gwamnati ba, kuma sauke su kwatsam na da hadari.

Labarai masu alaka