An kama 'yan Boko Haram a Nigeria

Hukumar tsaron farin kaya a Nigeria DSS ta ce ta kama wasu jiga-jigai a kungiyar Boko Haram da su ke shirin kai hare-hare a sassan kasar daban-daban.

Wata sanarwa daga hukumar ta ce an kama wani shugaban kungiyar ta Boko Haram mai suna Mudaisiru Jibrin wanda aka fi sani Namakele a unguwar Sauna a Kano.

Sanarwar ta ce Mudaisiru shi ne sabon kungiyar a Kano, kuma shi ne ya kitsa harin da aka kai makarantar sikandaren gwamnati a kauyen Mamudo a jihar Yobe a shekarar 2013.

Sanarwar wacce kakakin hukumar ta DSS Tony Opuiyo ya sanyawa hannu ta ce an kuma kama wasu mutanen hudu a unguwar Muazu a Kaduna , cikin su kuwa har da wata mace, a lokacin da suke shirin kai hare hare a jihar ta Kaduna.

Tony Opuiyo ya ce an kuma kama wani Aikhoje Moses a jihar Edo, wanda ya ke barazanar kai hare-hare ga jami'an diplomasiyyar kasashen waje dake Nigeria da kuma ofisoshin su, ciki kuwa har da jakadun Denmark da Switzerland.

Sanarwar ta ce an kuma kama wasu da ake zargi da aikata miyagun laifuka da suka hada da masu garkuwa da mutane da masu satar shanu.

Labarai masu alaka