Buhari ya yi tur da kisan mutane a Mafara

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari, ya yi tur da kisan wasu mutane takwas da aka yi a lokacin wani tashin hankali da ya faru a garin Mafara ta jihar Zamfara.

A cikin wani sako a shafinsa na twitter shugaban ya bayyana lamarin da cewa aikin rashin imani ne, kuma ya ce zai tabbatar da cewa doka ta yi aikinta kan wadanda ke da hannu a tashin hankalin.

A ranar Litinin ne din da ya wuce ne wasu mutane suka kai hari kan gidan wani attajiri a garin na Mafara, bisa zarginsa da kubutar da wani dalibi da ake zargi da yin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) inda suka hallaka mutane takwas.

Haruna Shehu Tangaza ya samu zantawa da mutumin da aka kai wa harin a gidansa, Yusuf Tajiddeen, wanda yanzu ke karkashin kariyar jami'an tsaro:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka