Yan sanda mata na saka hijabi a Scotland

Hukumar yan sanda a Scotland ta sanar cewar al'ummomin mata musulumai za su iya saka hijabi a matsayin wani bangare na kayan aiki da yan sanda ke sakawa.

Wannan wani bangare ne na yunkurin da yan sandan Scotland din ke yi na karfafawa musulumai mata gwiwa wajen shiga aikin tsaro.

A baya dai Jami'ai da ma'aikata yan sanda na damar saka tufafin addini amma sanarwar ta kuma tabbatar da saka hijabi a hukumance.

Shugaban yan sanda, Phil Gormley ya ce ya kamata yan sanda su wakilci al'ummomin da su ke yi wa aiki.

Wannan mataki dai ya zo ne shekara 10 bayan hukumar yan sanda ta Metropolitan Police da ke london ya amince da saka hijab a matsayin wani bangare na kayan aikin da yan sandan ke sakawa.

Labarai masu alaka