Nijar: Tsaro ya inganta a jahar Diffa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption sojojin jamhuriyar nijar a diffa

Gwamnan jahar Diffa ta jamhuriyar Nijar, Malam Lawali Dan Dano,ya tabbatar da kura ta lafa a yankin.

Ya kara da cewa al'amurra na tafiya yadda ya kamata a daukacin yankunan da dakarun kungiyar Boko Haram suke kai hare-hare.

A kwanakin baya 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai wani hari tare da halaka mutane sama da 90.

Gwamnan ya ce an samo saukin kai hare -haren saboda gwamnati ta karfafa matakan tsaro a yankunan.

Labarai masu alaka