Nigeria ta amince da tsarin kasafin kudin shekara 3

Image caption Najeriya na fatan hakan zai daidaita faduwar da kudin kasar ya yi

A Nigeria, gwamanti ta amince da tsarin kasafin kudi na shekara uku, inda ta yi hasashen samun bunkasar tattalin arziki na kashi 4 cikin dari.

Najeriya na kuma fatan hakan zai daidaita faduwar da kudin kasar, wato Naira ya yi a kasuwar musayar kudi.

Gwamnati ta yi kiyasin farashin gaggan danyen mai zai zama $42 zuwa $50 a tsawon wannan lokaci.

Za a tura tsarin kasafin kudin na matsakaicin zango zuwa majalisar dokokin kasar, domin 'yan majalisar sun amince da shi.

Labarai masu alaka