Kotu ta ce mata Musulmi na da 'yancin sa Burkini

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mata musulmai sun yi farin ciki da hukuncin

Wata babbar Kotu a Kasar Faransa ta dakatar da haramcin sanya kayan nunkaya da ke rufe jiki ruf wato Burkini da wasu biranen kasar suka yi.

Musulmi mata ne dai ke sanya Burkini.

Kotun ta ce a bayyane take cewa harmcin da aka sanya wa mata na saka kayan a garin Villeneuve Loubet ya sabawa doka, kuma take hakkokin dan adam ne.

Hukuncin zai kuma iya shafar wasu garuruwan 30 da suka sanya irin wannan doka, to sai dai fa kawo yanzu hukumomin wasu garuruwa uku sun ce za su ci gaba da aiki da dokar ta hana mata sa Burkinin.

Kotun za ta yanke hukunci na karshe akan ko haramcin ya dace.

Wani Lauya da ke wajen kotun yace mutanen da aka ci su tara yanzu sabo da saka Burkini, na iya neman a biya su kudadensu.

Musulami da dama sun yi farin ciki da wannan hukunci.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International tuni ta yi maraba da hukuncin, inda ta ce ya kamata a yanzu hukumomin Faransa su dauki ko wane irin mataki na kare hakkin mata.

Labarai masu alaka