An yi boren kin gwamnatin Zimbabwe

Masu zanga-zanga Hakkin mallakar hoto
Image caption Jam'iyyun adawa 18 ne suka hadu dan yin wannan zanga-zanga.

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe ya ja-kunne masu zanga-zanga cewa irin guguwar sauyi na mulkin demokuradiyyar da ta kada a kasashen Larabawa ba za ta kada a Zimbabwe ba.

Shugaba Mugabe ya yi zargin cewa da hannun kasashen waje a rikicin da aka yi jiya Juma'a, a Harare, babban birnin kasar.

'Yan adawa ne suka suka shirya zanga-zanga, suna kira da a aiwatar da wasu sauye-sauye ga dokokin zaben kasar gabannin babban zaben da ke tafe a shekara ta 2018.

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar a birnin Harare.

Harwayau sun lakadawa mutanen da ke sanye da jar riga mai alamar jam'iyyar adawa dan karen duka.

Labarai masu alaka