Majalisa za ta binciki lamarin 'yan gudun hijira

Zaman majalisa
Image caption Zorro ya ce yakamat nan ba da jimawa ba a dauki mataki kan kayan abinci da ke jibge a bakin ruwa

A Najeriya, kwamitin da ke kula da 'yan gudun-hijira na majalisar wakilan kasar ya ce zai yi bincike a kan sauya akalar abincin 'yan gudum hijira.

Hakan ya biyo bayan zargin cewa wasu 'yan kasar na zagon-kasa ga kokarin wadata masu gudun-hijirar da abinci.

Kwamitin dai na maida martani ne ga zanga-zangar da wasu 'yan gudun-hijira suka yi, a wasu sansanoninsu da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Shugaban kwamitin, Sani Zorro ya ce gwamnatin tarayya ba ta maida hankali kan halin da su ke ciki, kuma an dogara ne da kayan agajin da kungiyoyin agaji na kasashen waje ke kawowa.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa jibge kayan agajin da aka shigo da su daga kasashen ketare a bakin iyakar Nigeria da ta ruwa, ya kara matsalar rashin abinci da kayan bukatu na 'yan gudun hijirar.

Labarai masu alaka