Philippines: 'Yan IS sun fasa gidan kaso

'Yan sandan kasar Philippines Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fursunoni 15 su ma sun arce daga gidan kason, baya ga mayakan IS 8 da aka 'yanta.

A kasar Philippines, wasu masu tsaurin ra'ayi da ke mubaya'a ga kungiyar IS sun fasa wani gidan-yari, inda suka 'yanta mayakansu akalla 8, ta hanyar kai hari kan wani gidan-kaso da ke birnin Marawi a kudancin kasar.

'Yan sandan yankin sun ce akalla mayakan masu tada-kayar-bayan na kungiyar Maute su 20 ne suka kai hari kan gidan-mazan ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kwace makaman da ke hannun gandirobobi.

A makon jiya ne aka kama masu tada-kayar-bayan, lokacin da aka same su da wasu rokoki kirar cikin gida, jibge a cikin wata mota.

Akalla Fursunoni 15 ne suka arce daga gidan-yarin, bayan mayakan kungiyar masu tsaurin-ra'ayin.

Mayakan kungiyar Maute dai sun yi kaurin suna wajen kai harin bam da sace mutane a yankin Mindanao, inda ake da musulmi 'yan kasa tsiraru.