Gabon: Bongo da Ping na ikirarin nasara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Bongo a gefen hagu, na Jean Ping a gefen dama

Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo da babban abokin hamayyarsa, Jean Ping, kowannensu na ikirarin shi ne ya yi nasara a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Bangarorin biyu na zargin juna da yin magudi a zaben.

Magoya bayan Mista Ping sun ce shi ne ya lashe kashi sittin cikin dari na kuri'un da aka kirga zuwa yanzu.

Sai dai, bangaren shugaba Ali Bongo ya ce shugaban ya kama hanyar samun wani wa'adin na biyu.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce hukumar zabe ce kadai za ta sanar da sakamakon zaben da ake sa ran samu a ranar Talata.

Mista Ping, tsohon shugaban Tarayyar Afirka, ya na neman kawo karshen mulkin da gidan Bongo ya shafe kusan shekaru hamsin yana yi a kasar.