'Hare-hare ta sama ya hallaka mutane 35 a Syria'

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti

Masu sa ido kan yadda tashe-tashen hankula sun ce fararen hula talatin da biyar ne aka hallaka a wasu jerin hare-hare ta sama a arewacin kasar Syria.

Hukumar dake sa idon kan kare hakkin biladama ta kasar Syria ta ce an yi lugudan wuta a kan kauyen Jeb el-Kussa inda aka hallaka mutane ashirin tare da jikkata hamsin.

An kuma bada rahoton mutuwar mutane goma sha biyar, lokacin da aka kai hari kan wata gona a kusa da al-Amarna.

A farmakin wanda aka fara kaddamarwa a makon jiya, tankokin yaki da dakarun da 'yan tawayen Syria ke marawa baya sun kwace ikon yankin daga kungiyar I-S, tare da yin arangama da mayakan Kurdawa na YPG da Amurka ke mara wa baya.

Kasar Turkiyya na son tilasta wa dakarun na Kurdawa da su janye zuwa gabashin kogin Euphrates .

Tana yaki da hare-haren Kurdawan a kudu maso gabashin Turkiyya.

Labarai masu alaka